BAKANDAMIYAR GUMURZU Kashi na hudu 4 Na Umar Abdulhadi Mati Ebook created by Shuraih Usman Published at www.hausaebooks.com.ng (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 31. Tungar da Basadaukiya taja a gaban sadauki salka shine yayi sanadiyyar tashin wata matashiyar ƙura tsayuwa tayi irin ta sadaukai mata hannunta na dama na riƙe da zabgegiyar takobi ta ɗorata akan kafaɗarta yayin da hannunta na hagu ke riƙe da faffadan madaidaicin ƙugunta ta zubawa sadauki salka daradaran fararen idanuwanta tana mai masa wani irin murmushi mai nuna tsantsar yadda dakai, haɗe da raina abokin gaba. Karon farko da ta buɗe baki ta fara magana cikin wata zazzaƙar murya sadauki salka baƙin dutse ko? To yau ko baƙin ƙarfe kake ni basadaukiya naci alwashin sai na ladabtar dakai ayaune watan jin kunyarka ya kama, ayau sai ka amshi hukunci na zaluntar ba'yin Allah da ƙwace musu dukiyoyi da kakeyi tabbas kai gagarabadau ne a wanan nahiya tunda ka gagari sarkuna, attajirai, matsafa, da sadaukai, ka maida dayawa daga cikinsu marayu wasu kayi sanadiyyar karyewar tattalin arziƙinsu dan haƙa ayau ni Basadaukiya sai na ɗaukar musu fansa saina sa zuƙatansu farin ciki saina sa ka zama abin dariya ga alummatai dake wanan nahiya saina... Tsawar da sadauki salka ya dakawa basadaukiya ce tasa ta dakata da maganar da takeyi, haƙiƙa sadauki salka ya gama fusata domin saboda tsananin fusata har wani baƙin hayaƙine ke fita daga hancinsa kamar ba ɗan adamba cikin wata kakkausar murya marar daɗin ji ya fara magana ke yarinya idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi sadauki salkan da kika sani a da bashiine ba a yanxu a gabanki azatonki bani bibiyar duk wani motsi naki, kina ''yar shekara goma yarana sun haɗu dake a dajin dake iyakar wanan ƙasa taku yayin da kika fita farauta kece mutum ta farko da kika mani ɓarnar da ba zan taɓa mantawa ba domin kin kashe mani ɗan'uwa yayin da kukayi arba har sukayi ƙoƙarin yi maki fashi tare da ƙoƙarin cire maki kyallen da kika rufe fuskarki tun daga nan na fara bibiyar alamuranki, bayan nan mun ƙara haɗuwa dake karo na biyu lokacin kina "yar shekara shabiyar a daji inda muka fafata ƙazamin yaƙi a tsakaninmu amma babu wanda yayi nasara daganan bamu ƙara haduwa ba sai yanzu da muka haɗu a filin wanan gasar kisani kamar yadda kikayi mummunan tanadi a kaina nima haka nai miki mummunan tanadi dan haka idan baki shirya ba ma ki shirya dan ga maza nan bisa kanki nan take sadauki salka ya zare wasu adduna guda biyu haɗe da kawarara wata uwar kururuwa wadda saida tasa "yan kallo suka rufe kunnuwansu batare da ɓata lokaciba ya fallo da zababbben gudu......BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 32. Saboda tsananin gudun da yakeyi har wata guguwa ke take masa baya, itakuwa basadauki zuba masa ido tayi tana mai masa murmushin mugunta ko zare takobinta batayiba saida ya rage baifi taku ukku ba sadauki salka ya isa inda Basadaukiya ke tsayeba sai ya daka wani wawan tsalle haɗe da ɗaga addunansa guda biyu sama cikin mugunnufin a niyarsa yayiwa Basadaukiya farat ɗaya ya yagalgala namanta, idan kayi duba ga duk wanda ke wanan fili zaga ya zazzaro idanuwansa cikin tashin hankali da kaɗuwadomin tuni sun saɗaƙas cewa ƙarshen Basadaukiya yazo saidai kafin wanan sara ya isa gareta cikin tsabar zafinnama kamar walkiya ta zare takobinta ta kare wanan sara cikin ƙwarewa da tsantsar jarumta ganin abinda ya farune yasa "yan kallo suka ɗau ihu haɗe da jinjina a gareta shi kuwa gogannaka wato sadauki salka ƙara fusatashi wanan ihun na "yan kallo yayi nan take suka ruguntsume da azabbban yaƙi cikin baƙin zafinnama tamkar walƙiya suke kaiwa junansu sara da suka kai hadama magara da kai duka haɗe halbi da kafafuwa nan da nan suka tashi hankalon filin su kuwa "yan kallo wanan faɗa annashuwa yasa su domin kuwa faɗane na mazan jiya wanda aka jima suna baƙin artabu haɗe turmutsutsu da mazaje, ganin an ɗauki lokaci ana wanan gumurxu babu wanda ya samu nasarar koda lakutar jikin ɗan uwansa... I ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 33. Ganin babu wanda yayi nasarar koda lakutar jikin abokin karawarsa ne yasa wanan jarumai biyu ƙara fusata haɗe da tunxura, fusatarsu da tunzurarsu ce tasa wanan yaƙi ya ƙara caɓewa haɗe da cukurkuɗewa kowanne daga cikinsu ya ƙara zage dantse haɗe da buɗewa abokin karwar sa salo-salo na ƙofofin masifar yaƙi cikin baƙin zafin nama da juriya ta ban mamaki suke kaiwa junansu sara da suka haɗe da dukan junansu hannu da ƙafa duk wanda aka kaiwa sarako suka yana kaucewa ko ya kare kafin ya maido martani sai kaga an kaimasa duka da hannu ko da ƙafa amma saikaga kamar walƙiya ya kare ko ya kauce cikin ƙwarewa da bajinta saikaga shima ya maida raddi da masifa tayi masifa wanan jarumai sukaga iya yaƙi yana neman zuwa ɗaya sai kowa ya fara tunanin canza salon yaƙi domin ya samu damar lahanta ɗan uwansa ba tare da an kai ruwa rana ba hakance tasa kowanne daga cikinsu himmatuwa haɗe da ƙara zage dantse wajan safkewa dan uwansa salo-salo na masifar yaƙi ana cikin wanan turmutsutsu ne sai Basadaukiya ta shammaci sadauki salka ta daka wani uban tsalle haɗe da juyawa a sama sau ukku sana ta dire nesa kaɗan da inda sadauki salka yaja tunga sana ta gyara tsayuwarta jaɗe da yin murmushin mugunta hade da raini wanda yake nuni da cewa wuyar aiki ai bama 'a faraba domin wanan yaƙi da sukayi kamar sharar fagene, shi kuwa sadauki salka wani irin kallo yayiwa Basadaukiya wanda ke nuni da cewa "wai wanan yarinyar dame take taƙamane" ba'ayi auneba sai ganin Basadaukiya akayi tayi shiga tsalle sama haɗe da ware hannayeta kamar mai fukafiki haka ta sulmiyo ƙasa tayi di dirar mikiya akan sadauki salka, baiyi aune ba sai ganinta yayi a samar kansa kafin yayi wani kyakyawan yunƙuri tuni ta kawo masa wani bahagumen sara cikin baƙin zafinnama ya kare amma kafin ya ankara tuni ta sanya gwiwar ƙafarta ta masa wani wawan duka a fuska duk da yayi ƙoƙarin kaucewa amma sai da tayi nasarar samu gefen fuskarsa wananne yasa sadauki salka yaji wani azababben raɗaɗi ya ratsa masa ƙwaƙwalwarsa duk da haka abin bai tsaya nanba domin kuwa Basadaukiya wulƙila jikinta tayi haɗe da juyowa ta ƙara kawo masa walfta kamar shaho... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 34. Kamar shaho haka Basadaukiya takaiwa sadauki salka safta duk da yayi saurin duƙewa haɗe da juyo hakan bai hana Basadaukiya samun damar yankanshi a kafaɗa ba kafin ta dire da ƙafafuwanta nesa kaɗan da inda sadauki salka yake, wanan tsananin jarumta da bajintar Basadaukiya ce tayi yasa "yan kallo wanda suka haɗa da alummar aljannu dodanni da mutane ihu haɗe da tafi su kansu hamshaƙan sarakunan da suke zaune a wanan fili saida sukayo mata jinjina domin ya burgesu matuƙa, shi kuwa gogannaka wato sadauki salka fusata yayi zuciyarshi ta ƙufulo gashin jikinsa ya mimmiƙe idanuwansa suka ƙara ja jijiyoyin jikinsa suka futo sukayi burɗa-burɗa idan ka ganshi a wanan hali da yake ciki zaka iya cewa yana ɗaya daga jikin manyan dodannin da suka halarci wanan gasa saboda gaba ɗaya ya rikiɗa cikin tsananin fusata da ƙunar rai ya shafa kafaɗarsa yaga jini cikin ransa yace tabbas ko yanzu aka raba wanan faɗa wanan tarin ar ta mani abinda babu wani sadauki da ya taɓa mani dan haka idan har ban mata kisan wulaƙanciba to bazan taɓa hucewa ba nan take ya gyara tsayuwarsa haɗe da wurgi da takobinsa yana mai yafito Basadaukiya alamun su gwada "yar ƙashi hakan tasa Basadaukiya ta fallo da gudu tana mai soke takobinta a jikin kubenta tana zuwa gab da sadauki salka ta daka tsalle da niyyar tayi masa ɓarin makauniya shikuwa sadauki salka tsawa yayi kyam yana kallonta sai ƙafarta tazo gab da sukarsa cikin baƙin zafinnama ya cafketa ya wulwulata sau ukku a sama sana ya fyɗata da ƙasa ya ɗaga ƙafarsa ya baketa saida tayi sama sana ta faɗo ƙasa cikin galabaita hannuta na dafe da ƙugunta ta yunƙura zata tashi amma ta kasa saboda tsanani buguwa da tayi nan take hankalin kowa dake wanan fili ya tashi murna ta koma ciki, sadauki salka ya nufi Basadaukiya yana tafiya cikin taƙama da fusata yana mai ɗaukar takobinsa haɗe da yi mata murmushin mugunta ganin irin murmushin da sadauki salka ke mata ne yasa ba shiri ta miƙe haɗe da ƙara zare takobinta domin ta tabbata in har ta bari sadauki salka ya isketa a wanan hali da take ciki kashinta ya bushe domin ranta kawai zai nema nan take ta ɗaga takobin ta ta buga wata uwar kururwa haɗe da fallowa da gudu hakan ce tasa shi (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 34. Kamar shaho haka Basadaukiya takaiwa sadauki salka safta duk da yayi saurin duƙewa haɗe da juyo hakan bai hana Basadaukiya samun damar yankanshi a kafaɗa ba kafin ta dire da ƙafafuwanta nesa kaɗan da inda sadauki salka yake, wanan tsananin jarumta da bajintar Basadaukiya ce tayi yasa "yan kallo wanda suka haɗa da alummar aljannu dodanni da mutane ihu haɗe da tafi su kansu hamshaƙan sarakunan da suke zaune a wanan fili saida sukayo mata jinjina domin ya burgesu matuƙa, shi kuwa gogannaka wato sadauki salka fusata yayi zuciyarshi ta ƙufulo gashin jikinsa ya mimmiƙe idanuwansa suka ƙara ja jijiyoyin jikinsa suka futo sukayi burɗa-burɗa idan ka ganshi a wanan hali da yake ciki zaka iya cewa yana ɗaya daga jikin manyan dodannin da suka halarci wanan gasa saboda gaba ɗaya ya rikiɗa cikin tsananin fusata da ƙunar rai ya shafa kafaɗarsa yaga jini cikin ransa yace tabbas ko yanzu aka raba wanan faɗa wanan tarin ar ta mani abinda babu wani sadauki da ya taɓa mani dan haka idan har ban mata kisan wulaƙanciba to bazan taɓa hucewa ba nan take ya gyara tsayuwarsa haɗe da wurgi da takobinsa yana mai yafito Basadaukiya alamun su gwada "yar ƙashi hakan tasa Basadaukiya ta fallo da gudu tana mai soke takobinta a jikin kubenta tana zuwa gab da sadauki salka ta daka tsalle da niyyar tayi masa ɓarin makauniya shikuwa sadauki salka tsawa yayi kyam yana kallonta sai ƙafarta tazo gab da sukarsa cikin baƙin zafinnama ya cafketa ya wulwulata sau ukku a sama sana ya fyɗata da ƙasa ya ɗaga ƙafarsa ya baketa saida tayi sama sana ta faɗo ƙasa cikin galabaita hannuta na dafe da ƙugunta ta yunƙura zata tashi amma ta kasa saboda tsanani buguwa da tayi nan take hankalin kowa dake wanan fili ya tashi murna ta koma ciki, sadauki salka ya nufi Basadaukiya yana tafiya cikin taƙama da fusata yana mai ɗaukar takobinsa haɗe da yi mata murmushin mugunta ganin irin murmushin da sadauki salka ke mata ne yasa ba shiri ta miƙe haɗe da ƙara zare takobinta domin ta tabbata in har ta bari sadauki salka ya isketa a wanan hali da take ciki kashinta ya bushe domin ranta kawai zai nema nan take ta ɗaga takobin ta ta buga wata uwar kururwa haɗe da fallowa da gudu hakan ce tasa shi sadauki salka ɗaga addunansa biyu ya fallo da gudu yana mai ruri mai tsorata ƙanan sadaukai tabbas du wanda ke wanan fili ya tsorata da wanan haɗiwa da za'ayi saboda sunsan cewa idan har akayi wanan haɗuwa dolene a samu matsala..... February 24 at 1:03 PM · Facebsadauki salka ɗaga addunansa biyu ya fallo da gudu yana mai ruri mai tsorata ƙanan sadaukai tabbas du wanda ke wanan fili ya tsorata da wanan haɗiwa da za'ayi saboda sunsan cewa idan har akayi wanan haɗuwa dolene a samu matsala..... February 24 at 1:03 PM · BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 36: Haƙiƙa ba ƙaramin tashi hankalin waɗanan jarumai ba yayi ba komai yasa hakan ba face ganin wankin hula na ƙoƙarin kaisu dare hakance tasa kowanne daga cikinsu ya ƙara fusata kamar hadin baki nan take kowanne daga cikinsu yayi watsi da makamin dake hannunsa hakanna faruwa basadaukiya ta dunƙuƙe hannunta haɗe da kwantsama wata uwar kururuwa ta falfalo da azababban gudu tana mai tunkarar sadauki salka cikin mugunnufin ayita ta ƙare saboda tsananin ƙarfin gudu da take ne yasa har wani tashi sama take, ganin hakance tasa sadauki salka shima ya dunƙuƙe hannunsa haɗe da kwarara wata uwar kururuwa yana mai dukan ƙirjinsa da hannuwa biyu kafin ya fallo da gudu shima zuciyarsa cike take da mugunnufi suna kusan haɗuwa sai kowanne daga cikinsu ya dako uban tsalle yana mai kaiwa ɗan uwansa mugun naushi kowanne cikin zafinnama ya kare kafin su silmiyo ƙasa suna dira suka kacame da wani azababben yaƙi "mai taken ƙarshe tika tik" haka suka dunga jibgar junansu kamar jikinsu ba na jini da tsoka bane ana cikin wanan baƙin gumurzu ne sadauki salka ya shammaci badaukiya ya gabza masa wani mummunan nashi a ciki kamar a janyeta haka tayi tsalle ta tumu da ƙsa a can gefe tana mai dafe cikinta cikin galabaita domin ko numgashinta ma da kyar yake fita kafi ta dawo cikin hayyacinta ne sadauki salka ya ƙara dako tsalle daga inda yake ya ƙara shaƙar wuyanta yana mai ɗagata sama nan take ta fara wutsul-wutsul tana mai kakarin mutuwa tabbas wanan shaƙa da sadauki salka yayiwa basadaukiya bata wasa bace ya kalleta yana mai mata wani murmushi mai ɗauke da tsabar xunxurutun mugunta ya fara maga cikin izza ''hm haba yarinya waya faɗa maki ana zama wani a banza, azatonki a banza na buwayi sarskuna,matsafa,sadaukai da jarumai na wanan nahiyar tabbas a yaune zan zare maki numfashinki sai na miki kisa mafi muni wanda a tarihin duniya ba'a taɓa yiwa wani irinshiba yana zuwa nan a maganarsa ya ƙara shaƙeta nan take idanuwanta suks fito numfashinta ya sarƙe ta fara jiyo ƙamshin mutuwa ganin haka yasa alƙalan gasasuka fara shirin kaɗa ƙaraurawar da ke nuni da tsayawar wanan gasa sadai kash! Adaidai lokacinne sadauki salka ya jimƙe hannuwansa na hagu nan take wata koriyar wuta bayyana, bayyanar wanan koriyar wuta ce yasa kowa dake wanan fili ya tsorata yana mai dafe ƙirji domin duk wanda yasan labarin sadauki salka to yasan bala'in wanan wuta tasa domin da wanan sirri na koriyar wutane ya fitini sadaukan jinsin mutum, aljan, kai hadama dodanni ...BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 37. Ganin wanan koriyar wuta yasa sarki nawwar saurin miƙewa kafin hannun sadauki salka ya isa kan basadaukiya tini sarki nawwar ya nuna sadauki salka da yatsarsa nan take wata iska mai ƙarfi ta suri sadauki salka ta yi hajijiya dashi sana ta damfara da ƙasa ganin hakane yasa yaran sadauki salka wanda suka shiga cikin "yan kallo suka saje dasu tashi tsaye haɗe da zare makamansu saidai kash basu samu damar ida nufinsu ba suka ja suka tsaya cak sakamakon tsawar da sukaji haɗe da rugugi inda ƙasa ta rinƙa girgiza kamar zata rufta ganakace taba filolin da suka tokare rufin da ya zagaye fadar fara zabtarewa suna danne "yan kallo duk wanan bai isaba bayyanar baƙar inuwar data lulluɓe dukkan filin ita ta ƙara sa "yan kallo durƙushewa inda wasu suka faɗi haɗe da dunƙulewa waje ɗaya cikin firgici da kaɗuwa haɗe da tashin hankali hakance tasa suka ɗaga kawunansu domin ganin masifar da ta haifar da wanan bala'i abinda suka ganine yasa su ƙara gigicewa haɗe da firgicewa wanda dayawa daga cikinsu saida sukayi danasanin ɗaga kawunansu sama da sukayi shikuwa uban gayyar wato sarki nawwar tashi tsaye yayi karon farko da tsabar tsoro da tashin hankali ya bayyana a fuskarsa ganin mawuyacin halin da mutanensa suka shigaba shiri ya tafa hannayensa nan take baƙin labulen da ya nannaɗe kansa tun farkon wanan gasa ya ƙara bayyana yayiwa "yankallo hijabi , sukuwa manyan gayyar ko a jikinsu wai an nyakushi kakkausa ƙara gyara zamama sukayi sadai dakarunsu da suka zo gabansu suka ja daga suna masu raba idanuwa saboda tabbatar da tsaro .... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 38. Bakomai ne yayi sanadiyyar afkuwar wanan bala'in ba face bayyanar haɗaɗiyar baƙar rundunar da ƙunshi jinsin mutum dana aljan babban abin tashin hankali haɗe da firgici ga wanan baƙar runduna shine baƙin Ƙaton mummunan aljani dake jagorantar wanan baƙar runa domin duk wanda ya kwana ya tashi a duniyar hatsabibanci da jarumta to yasan aljani FARGAM aljani da baya domin baya da shekara sittin da biyu shike riƙe da kambun jarumtar na duniyar baƙaƙen aljannu tabbas dole sunan aljani fargam ya watsu a duniya idan akayi duba da irin gwagwarmayar da ya jima yanayi da hatsabibai, duk da sarki nawwar ya sanya shaki na labulayen tsafi tsakanin "yankallo da aljani fargam amma kallon farko da "yan kallo suka masa saida yasa dayawa dsga cikin sumewa masu ƙaramin ciki kuwa sukayi ɓarinsa, masu ƙarfin haline daga cikinsu ne suks durƙuce haɗe da ƙara dunƙulewa waje ɗaya tabbas kallon aljani fargam ma kanshi babban tashin hankaline ga ƙananun sadaukai cikin murya mai amo wadda take ɗauke da tsantsar amon izza da buwaya irin ta mazajen jiya ya fara magana cikin isa da taƙama "sarki nawwar mai daular ruma sarkin dake burin zama sarkin- sarakan duniya, tabbas ka ɗebo ruwan dafa kanka kaɗebo wa kanka aikin da yafi ƙarfin ka duk da cewa duniya ta shaida kaima sadaukine kuma hamshaƙin matsafi wanda ake damawa dashi a duniyar tsatsuba, amma kasani ba'a zama sarkin sarakai a banza kuma kana zaune a gida ko sarki sahibul kairi bai kai wanan matsayiba saida ya bar karagarsa, ƙasarsa, ya shiga duniya yayi gwa-gwarmaya da hamshaƙan baƙaƙen aljannu da mutane wanda suka amsa sunansu hatsabibai kuma gawurtattu kamar irinsu sarki BARUSA da matar sana ya kai wanan mataki sai kai kake tunani da sa rai cewa zaka taka wanan matsayi kana zaune a gida haƙiƙa kayi kuskure duk da cewa ka taɓuka wani abu saidai kuskurenka ɗaya shine da ka sanya yaudara da ha'inci a cikin lamuranka da bokanka wanan shine babban kuskuren da kuka tafka kai da bokanka... Happy juma'at kareem.BAKANDAMIYAR GUMURZU. Chapter 39. Nasan zakayi mamakin ta yadda nasan wanan babban sirri naka duk da cewa kayi amfani da da layarka ta ɓata wajan ɓoye wanan sirri wadda a tunaninka idan har kayi amfani da ita kaf duniya babu wani mahaluki da zai iya wanan sirri naka wananne dalilin da yasa ka tara wanan hamshaƙan sarakunan da matsafa, jarumai daga sassa daban daban na duniya duk da cewa kowannensu saida yayi bincike akan wanan gasar kafin ya taho amma babu wanda ya samu damar ganin wanan sirri naka tabbas wanan sarƙa taka tana ɗaya daga cikin abubuwa biyar mafi daraja a duniya, hm!! amma idan kayi duba da matsayin da na taka a dunuyar tsatsuba wanan ba komai bane kasani shi ilimin tsafi kogine da kowa ke kamfato iyakar iyawarsa ba dole bane abinda na ɗakko yayi daidai da wanda ka ɗauko ba wanan ne dalilin da yasa tun lokacin da aka fara wanan gasa nake bincike akanta daga ƙarshe na gano akwai wani babban sirri dake ƙunshe da ita yayin da na matsa bincike sai na gano babu yadda za'ayi in gano wanan sirri sai na haɗa jinin jinsi huɗu na zubashi a kwatarniyar tsafina sana in haska wanan jinin da madubin tsafina sana inga wanan sirri gani hakane yasa na nazo wanan birni a sirrance na haɗu da aljana zabariyya, daga jinsin dodanni kuwa na nemo su dodo zalƙim, jinsin mutane na nemo sadauki saljam na musu bayani komai inda suka amince kowanne ya zuba jininsa a wanan kwatarniya tawa ta tsafi sana muka kamo wani bijimin zaki muka yankashi mua zuba jinin sa a wanan kwatarniya hakan na faru sai na fiddo maɗubin tsafina na haska wanan jini hakan na faruwa sai ga hotonka da na bokanka yayi da kuke tattunawa akan tsafin ds kake so ka haɗa wanda zaka zama sarkin sarakuna ka gallabi .mutum ɗa aljan daga wanda hakan bazai yiwuba har sai kun mallaki jini, ɓallen ƙashi, da haƙoran manya-manyan sadauksi da hatsabiban jaruman da suka gagari duniya a wanan zamanne kuka samu matsayar cewa zaku aika takardar gayyata zuwa ga sadaukai jarumai da manya-manya hamshaƙan sarakuna... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI) BAKANDAMIYAR GUMURXU. Chapter 40. Kai ya isa haka sarki nawwar ya dakawa aljani fargam tsawa cikin wata kakkasar murya mai cike da tsabar ɓacin rai da fusata haɗe da hasala idanuwansa sunyi jawur jikinsa sai tsuma yake karon farko da sarki nawwar ya fara magana cikin murya mai amo" Haƙiƙa ka cika hatsabibi Kuma tantiri da lokaci ɗaya ka tono babban sirrin da na jima ina ɓoyewa, ka cutar dani ka katse mani babban burina na duniya, hakika kayi nasarar tsaida wanan gasa ,saidai baka isa ka hanani cika wanan burin ba duk rintsi duk tsanani koda zatakaimu ga yaƙar juna sai na ida cika burina a yanzu na mallaki ballen ƙashin sadauki salka lokacin da aka karyashi a ƙafa, inada haƙorin aljana zabariyya yayin aljana zulma ta nausheta haƙorinta guda na gaba ya fita , ina da ɗigon jinin dodo zalƙim da dodo kalkus yanzu abin da ya rage shine in mallaki aɗigon jini shahararrun jarumai na guda ukku wanda suka fito daga dauloli ukku sune daular hindi,daular asiya,daular kisra, A yanzu haka ina da ɗigon jinin sadauki salka wanda kowa yasan hafaffen ɗan daular habasha ne sai kuma jini basaudakiya wanda ita kuma kowa yasan haifaffiyar daular rumawace, waɗanan dauloli sune dauloli mafi girma da ƙarfi, yawa da shahara a duniya idan har na kammala haɗa wanan abubuwane zan haɗa da jini na dana matata sana ina haɗa da farin ƙarfe mai daraja ta farko a duniya wanda ake haƙowa a ƙasar kogin nil wanda tuni na mallakeshi in sana'anta KARAGAR MULKI wanda duk wanda ya hauta sai ya shahara, ya tumbatsa, ya gallabi al'ummar mutane data aljannu kai hadama dodanni sai ya kafa tarihin da har duniya tanaɗe baza'a daina tunashi ba, sai ya kasance sunansa kaɗai aka faɗi sai mutum ya girgiza sai ƙowani sarki da ya shahara a duniya yazo ya durƙusa gabansa, sanan babu wanda ya isa ya hau karagar sai jinina... " kai!!! dakata ya isa haka sarki alkasim ya katse sarki nawwar cikin murya mai cike da ƙarfin izzar mulki da tsabar jarumta ya fara magana....