BIRNIN AZZALUMAI Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz Sani M Gini Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com BIRNIN AZZALUMAI 2 Littafe na biyu . Completed book 2 Na ABDULAZIZ SANI. Typing.. By Suleiman zidane. Dajin haka sai lasmir ta mike da sauri ta shige cikin gidan, shi kuwa tsoho husam sai yazo ya zauna daf da jarumi zauna. Duk su biyun sai suka yi shiru har izuwa tsawon wani lokaci na yan dakiku. Daga can sai jarumi zaunal yai gyaran murya yace, ya kai Abba lasmir! Ina son nayi maka wata tambaya idan har baza ka samu damuwa ba. Husam ya numfasa yace, fadi tambayarka ko wace iri ce, ya kai dana domin tambaya ita ce tafarkin neman ilimi. Jarumi zaunal ya ce, wai shin menene dalilin da yasa sarki baskar ya raba ku da mahaifiyar lasmir? Sa'adda tsoho husam yaji wannan tambaya sai yayi shiru kamar ba zai ce komai ba kuma nan take idanunsa suka kada suka ciko da ruwan kwallah. Daga can sai yadubi zaunal yace, yaro kayi mini tambayar labari mai tsawo amma zan yi kokari gajarce maka shi. Asalin sarki baskar abokina ne kuma aminina wanda muka taso tare tun muna yara kanana. Mahaifinsa Da mahaifina ma haka suka taso aminan juna. Typing. Suleiman zidane. Mahaifina ne sarkin birnin Azzalumai, shi kuma mahaifinsa shine sarkin yaki. Tun iyaye da kakanninmu tsawon shekaru da dama ake rayuwa ta zalunci a wannan birni namu, ya zamana cewa sarakuna basa adalci ga talakawansu. Masu arziki da masu karfin jarumtaka kadai ke iya kare kansu daga harin masu karfi, barayi da mazalunta. Abin ya zamo tamkar al'adar awannan birni namu. A gaban mutane za'a yiwa mu'2 kwacen dukiyars ko matarsa babu wanda zai taimakeka ko yayi yunkurin ya hana. Sai idan mu2 yai sa a ne ma zai tsira da rayuwarsa. Mutanen wannan kasa tamu sun kasance basu da alkawari, amana da gaskiya don haka duk yadda kake da mu2 zai iya cin amanarka ya cutar da kai. Hakan ce masa kowa bai yarda da kowa ba. Sarki bai yarda da eadawansa, hadimansa da dakarunsa ba. Haka zalika, miji bai yarda da matarsa ba kai hatta tsakanin bayi da iyayen gijensu babu yarda da amana amma wani babban Abin mamaki sai gashi ni da sarki baskar babu wannan rashin yarda tun daga har izuwa lokacin da muka gaji iyayenmu. Lokacin da na zamo sarki, shi kuma ya zamo sarkin yakina sai da kowannenmu ya shekara biyar akan mulkinsa ba tare da munyi aure ba. Haka yasamo asali ne da tsoron irin matan da zamu aura don gudun kada a hada baki dasu a ci amanarmu. Sau uku yan majalisar kasar suna zaman taro akan yazama wajibi mu nemo matan da zamu aura domin mu sami magada, in ba haka ba kuwa saidai muyi murabus akan mukamanmu. Nan take majalisar ta yanke hukuncin cewa ta bamu watanni uku kacal mu nemo matan aure in ba haka ba kuwa mu ajiye mukamanmu da hannunmu. Lokacin da muka ji wannan hukunci da majalisa ta yanke sai hankalinmu ya dungunzuma ainun, muka rasa abinda ke mana dadi. Typing. Suleiman zidane. Sai da muka shafe sa'a uku muna nazari da tunanin inda zamuje mu nemo matan aure. A karshe dai muka yanke shawarar cewa zamu tafi izuwa wata nahiyar ta daban, mu Inda basu da al'ada ta zalunci da rashin amana, mu samo matan aure mu dbwo kafin cikar wa adin da aka dibar mana wato wata uku ya cika. Ba tare da bata wani lokaci ba sai muka sanar da majalisa hukuncin da muka yankewa kanmu. Koda jin haka sai yan majalisar suka kamu da tsananin farin ciki. Nan take aka shirya mana guzuri muka hau ingarmun dawakai aka yi mana rakiya har izuwa karshe gari. A wannan lokaci kusan gaba dayan mutanen gar ne suka yi mana wannan rakiya, maza da mata, yara da manya. Yan mata da zawarawa kuma kuka suka rinka yi sbd babu wacce ta zama gwana a garemu, bare mu zabeta a matsayin matar aure. Bisa tarihin wannan masarauta tamu ba'a taba samu masu mulkin da suka auro baren mace ba daga wani garin koda wata nahiyar dabam, don haka ni da sarkin yaki baskar mun zo da sabuwar al'ada ne. Haka dai muka yi ban kwana da jama'ar tamu muka sakarwa dawakanmu linzamai muka nausa cikin daji. Abinka da zaratan jarumai wadanda suka takama da sadaukantaka iya Yaki gami da karfin sihirin tsafi, kai tsaye muka rinka kutsawa cikin dazuzzuka iri-iri ba tare da shakkar wata halitta mai rai ba. Sai da muka shafe kwanaki goma sha daya muna keta dazuzzuka bata re da mun riski wani gari ba kuma duk sa'adda muka hadu da wani mugun abu walau mugayen dabbobin daji ko wasu gawurtaccin yan fashi ko mugayen aljannu, farat daya muke tarwatsasu mu kashe na kashewa, masu gudu kuwa su tsere..... DALILIN DA YASA FARIN CIKI GIDA KODAN INTSIRA DA RAYUWA.. To Kuma shin inkuka gana juya zaku jiyo ne kokoh sai kun ganu makamu azabban yaki dazai faru.. Saikuma anjima... Kuyi comment................. BIRNIN AZZALUMAI 2 PART -B- Na Abdul AZIZ SAni. Typing. Suleiman zidane. Daya muke tarwatsasu mu kashe na kashewa, masu gudu su tsere. Mahaifin baskar ne ya koyar damu yaki tun muna kuruciyarmu kawo izuwa girmanmu. Tsafi kuwa mahaifina ne ya horar da mu. Nida baskar bamu taba yin cacar baki ba bare mu jarraba jarumtakarmu akan juna. Kai sbd tsananin kauna da son juna, dayanmu a shirye yake ya sallama rayuwarsa don kare ta dan uwansa a duk lokacin da wani mugum abu ya tunkaro mu. Kowa a cikin birnin azzalumai yana mamakin irin amanar dake tsakaninmu gami da kaunar juna alhalin muna rayuwa a garin da kowa bai yarda da kowa ba. Suleman zidane kenan. Komai yawan dukiya idan muka sameta, burin dayanmu ya barwa dayan. Duk tsananin hadarin wuri idan muka zo zamu shige sai kaga gardama takarke, kowannenmu na cewa shi zai fara shiga dan kare lafiyar dan uwansa da rayuwarsa. Bisa wannan dalili ne labari amanarmu da abotarmu ta bazu ko'ina a nahiyar tamu, ya zamana cewa babu inda lbri nmu baikai ba. Nahiyar da muka tunkara bamu santa ba kuma bamu taba zuwanta ba, don haka a lokacin da muka fara shiga cikin dazuzzukan nahiyar sai muka kamu da matukar mamaki gami da farin ciki bisa tsintar kanmu a cikin dazuzzuka masu irin yanayin da bamu saba gani ba. (to nima fa haka zai kasance cikin farin ciki idan naga kunayi comment dan hakane zakara min kwarin gwiwa dan irinka cigaba da muku post wanda yafi wanda nakema ku abaya yawa..) Tabbas wadannan dazuzzukan sun fita dabam da irin dazuzzukan dake nahiyarmu sbd tarin arzikin dake cikinsu bishiyoyi da koramai da tsirrai masu yawan gaske. Tun a farkon shigarmu nahiyar muka tsaya cak muna kallon irin tarin ni'imar dake cikin dajin muna mamaki da murna. A wannan lokaci ne sarkin yaki baskar ya dubeni yace, yakai abkna, kayi sani cewa tabbas ba za a rasa mafarauta ba a cikin wannan daji daga nahiyoyi dabam-dabam sbd tarin wannan ni'ima dake cikinsa. Nikaina da ban kasance mafarauci ba sai naji ina sha awar ace na zauna a wannan wuri iya tsawon rayuwata. Koda naji wannan batu sai na tuntsire da dariya sannan nace, ai komai dadin dake anan bai kai gari ba. Ni a matsayina na sarki mai mulkin mutane ya za'ayi na ji dadin mulkar dabbobi da aljanu? Da jin haka shima baskar ya bushe da dariya yace tabbas kayi 2nani mafi kyau ya shugabana. A wannan lokaci da muke yin wannan hira rana ta fadi, magariba ta doso kai, don haka sai sarkin yaki baskar ya dubeni yace ya shugabana ina ganin cewa zai fi kyau mu yada zango a cikin wannan daji mu kwana anan sbd akwai alamun hasken farin wata, in yaso da safe sai mu cigaba da tafiyarmu. Koda jin wannan shawara sai nayi na.am da ita na dube shi nace, to ai sai mu dan kara gaba domin mu nemi wurin da ya dace mu yada zangon. Ba tare da wata gardama ba sai baskar ya amince da wannan shawara da na kawo. Nan take muka kara gaba muna tafiya a hankali, dawakanmu na sassarfa tamkar bama sonyi sauri. Tafiyar da mukayi bata wuce ta dakika dari hudu da s 3ittin ba sai kawai muka hango wata bukka a tsakiyar dokar daji. Koda hango wannan bukka sai muka ja linzamin dawakanmu muka tsaya cak. Tsowan yan dakiku sannan baskar ya dubeni ya ce waccan bukkar ta wani mafaraucin ce kuma gawurtacce mai ji da kansa. Dubi yadda ya bar bukkar tasa a bude ko rufeta bai yi ba kuma ga alama bbu wata halitta da tayi yunkuri shiga. Duk yadda akayi mashahurin matsafi ne koda jin haka sai nayi dariya na ce, ai kuwa yau wannan mafarauci ya gamu da gamonsa. Phone number. 09064179602 mu shiga cikin bukkar tasa muyi abinda muka so sarkin yaki baskar yayi murmushi ya ce, an gama ya shugabana. Nan take muka durfafi wannan bukkha kai tsaye ba tare da shakkar komai ba. Kafin mu sami nasarar shiga cikin wannan bukkar sai da mukayi bakin gumurzu da wadansu bakaken aljanu har kowanenmu ya sami dan rauni a jikinsa. Ni akan damtsen hannuna na dama shugaban aljanun ya yankeni da farcen hannunsa, take wurin ya dare, jini yai tsartuwa. Cikin fushi na fill e masa kai. Shi kuwa baskar akan cinyarsa ta hagu aka sare shi kurma ihu sakamakon zafin da yaji. Suleiman zidane. Kuringa comment and like. Hakan ne ya fusatamu muka ragargaje aljamun a cikin dakiku kadan sai kususuwansu muka zube a gaban bukkar. Nan take kuma muka shige cikin bukkar. Amma ni suleiman zidane sainaki shiga sbd tsaro. Da shigarmu muka iske dukiya ta dinare mai yawa tsubi.tsubi kuma muka ga lafiyayyen abinci da gasasshen nama mai dumi ga dukkan alamu ma ba'a dade da gasa naman ba. Danasa ni ni zidane na bisu dadani za aci dadi nan amma rashi sani yafi dare duhu.. Abkai. Nan dai muka shafa magani sannan muka afkawa wannan abinci muka cinye komai. Hatta kashin naman sai da muka tsotse. Bayan mun gama kimtsawa sai muka kishingida muna hutawa tamkar a cikin idan sarautarmu muke ba tare da shakka ko tsoron komai ba. Abinka da wadanda suka sha doguwar tafiya sannan muna dauke da matukar gajiya, sai nan da nan barci ya sace mu.... kaico! rashin saniyafi dare duhu..... A Nan zai tsaya sai kuma in Allah yakai mudasafe zakuji cigaban kurin ga comment dan irin ga yi post mai yaw a...... Happy Juma.at Khareem BirNIN AZZALUMAI 2 Part C na abdul aziz sani, typing. SuleimanPart C na abdul aziz sani, typing. Suleiman zidane tex ya isawa zidane cewa.. Kawai sai muka ji kamar a mafarki an daka mana tsawa mai matukar firgitarwa tamkar saukar aradu. A firgice muka farka muna masu mikewa zaune zumbur. Koda muka yi arba da wanda ake tsaye gabanmu a kofar bukkar, sai muka kame tamkar wasu gumaka. Ba komai bane yasa muka fada cikin wannan hali ba face tsananin mamaki gami da dimaucewa ba wai tsoro ba. Wata tsaleliyar buduwar ce ta gaban kwatance wacce za'a iya kiranta da sunan shugabar kyawawa ta duniya. Tsaye a gabanmu fuskarta a murtuke har tana gatsine sbd tsananin fishi tana sanye da riga da wando na fadar damisa. Matsattsu wadanda suka tona asirin kyawon surar jikinta. Surar da bbu wani lafiyayyen namiji da zai yi arba da ita batare da ya dimauce ba. Tana ruke da wani baka na musamman mai matukar kyau da tsadar gaske. Ko a sarakai ba kowa ke da mallakin irinsa ba. A gadon bayanta kuwa ta goya Jakar kibbau. A kallah za a iya samun kibiyoyi dari a cikin jakar. A kuibin cinyarta ta hagu wata zabgegiyar takobi ce a daure, wadda kufenta ma da zinare aka yishi. Wohoho! Idan mai kyau yayi ado da abu mai kyau sai kaga kyawu ya kure kansa. Nidai suleiman zidane kamewa nayi nakasa daina typing.. Dan banma san kome nake rubutawa sbd da tsabage kyauwunta. Duk da irin tsananin jarumtakarmu da rashin tsaronmu sai da muka dan firgita sbd kwarjinin wannan kyakkyawar jaruma da kuma irin kirarta ta manyan sadaukai. Mun sha haduwa da zaratan mazaje wadanda suka fita kwarjini da kirar sadaukantaka amma basu razanamu ba kamar ita ba. Cikin kakkausar murya, duk da cewa akwai zaki a cikinta tamkar zuma, ta dubemu ta ce, su waye ku? Menene takamarku har zuku zo ku kashe masu gadin bukkata kuma ku cinye mini abincina? Don samun wuri da raini harma kuma barci a cikin bukkata! Na rantse da darajar tsafaffina yau sai kun raina kanku kuma sai kunyi nadamar wannan babban kuskure Da ganganci da kuka tafka. Koda jin wannan muka bushe da dariyar mugunta a lokaci da guda. Ko lala bata ce mana ba sai kawai ta zuba mana ido tana kallonmu gami da sauraron abinda za muyi. Kawai sai na mike tsaye na dubeta nace, ni sunana sarki husam mai mulkin birnin azzalumai. Wannan kuma sunnansa baskar kuma shine sarkin yakina. Yake wannan mafarauciya! Kiyi sani cewa sarki a duk inda yake yana da ikon taba dukiyar kowa. Don haka sai kiyi godiya bisa amfanin da nayi da bukkarki da abinciki kuma ki nemi gafarata bisa daga muryarki a garemu kafin fishina ya tabbata a gareki. Ki sani cewa idan kika yi ladabi da biyyaya zan biyaki da dukiya ninki dubun wacce kike da ita a cikn wannan bukka.. Kafin nagama fadin abinda ke bakina tuni kykkawar buduwar ta tari numfashina tana mai daka mini tsawa a karo na biyu ta ce, kar kudameni db surutun banza. Idan kun cika mazaje to ku fito ku kare kanku. Tana gama fadin haka sai ta zare takobinta, ta yafutomu da hannu. Sai baskar ya sha gabana ya tare ni da hannunsa, ya ce haba ya shugabana! Ai sai ta gama db yaronka sannan zaka sa hannu. Yana gama fadin hakan sai shima ya zare takobinsa ya tunkari budurwar ya nufeta gadan-gadan da dukkan karfinsa ya kai mata wawan sara. Tab injan rashi sani yafi dare duhu daya san abinda zai biyo bayada baiyi wannan gangaci ba inji zidane nedai ina cin kan bishiya iya na leke kumai ke farawa ina rubuta muke hata in asukayi tari ina rubutawa gaskiya ni mafa jarumine bansaniba... Cikin bakin zafin nama ta kaucewa saran takobinsa ta shafci kasa. Kafin yayi wani yunkurin ta makeshi da karfarta ya kife kasa sumamme. Sbd tsananin kaduwa da mamaki sai nakasa motsawa. Ban taba ganin mace mai zafin nama db karfin duka ba kamar taba. Lokacin da jaruma zamirata ta make sarkin yaki baskar ya kife kasa sumamme, ya zamana cewa an fara kallon-kallo tsakaninta da sarki husam. Cikin zafin nama sarki husam ya mike zumbur yana mai gyara tsayuwarsa ya fito daga cikin bukka yana mai taka sawunsa a hankali cikin sanda tamkar barawo na neman sa'a. Hmm nidai zidane abin dariya ya ban... Sai daya samar da tazara a kallah taku goma a tsakaninsa da jaruma zamirat sannan ya tsaya cak ya fuskanceta sosai koda ganin haka sai zamirat tayi masa dan gundun murmushi tace a ranta... GA DUKKAN ALAMU WANNAN SARKI ZAIFI SARKIN YAKINSA JARUMTAKA DA IYA YAKI. DON HAKA BARI MU ZUBA MU GANI DON SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARA.. Kafin sarki husam ya sake fadin wani abu, tuni zamirat ta dako tsalle sama daga inda take tsaye tamkar daga cikin baka aka harbota ta kowa masa mugun sara akan kafadarsa da nufin ta gargeshi gida biyu. Cikin zafin nama yasa takobinsa ya kare sara. Sbd nauyin saran da karfinsa sai da ya durkushe kasa bisa gwiwarsa a lokacin da tartsatsin wuta ya tashi sakamakon ya dago sama ya danna takobinsa iya karfinsa akan tata sai gashi yana tarata baya kafafansu na tura kasa tana kokarin dagowa sama gami da tsaidasu amma ta kasa. Nan take ta gane cewa tabbas ta gamu da gwarzon namiji. Haka dai muka cigaba da baya muna tirjiya akan kasa muka tayar da kura a wajen har muka dbngana izuwa jikin wata bishiya. Damar da zamirat ta samu ta tsaya cak, sai ta wurlila jikinta suka yi katantanwa a tare suka ci gaba da azababben yaki ya zamana cewa muna kaiwa junanmu sara da suka cikin tsananin kwarewa da jarumtaka ta ban al'ajabi. Wohoho! Idan gwani da gwani suka hadu suna gumurzu kallo yafi dadi, amma kuma cikin tashin hakali da firgici... Dalilin dayasa ni suleiman zidane kenan nasauko daga kanbi shiyarda nake kallon gumurzu kenan na falfala da gudu ne cikin daji kenan... Sai kuma kura talafa zuwa anjima zandawo.......kuyi comment...fa. Inkuna so nadawo da wurin inba haka ba sai ta allah kuma dan bazadawo ba dan kar tsautsayi ya gifta dani..... ...