KOGON ANNOBA Littafi na Daya 1 Na Mansur Usman Sufi Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com KOGON ANNOBA Part A Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Mansur Usman sufi Kananan yara ne mace da namiji kyawawa na gaban kwatance ke ta faman tsala matsanancin gudu babu sassauci saboda tsananin gudun da yaran keyi idan kagani sai kayi tsammanin zasu fita daga duniyar ne, kai duk sa'adda suka waiga bayansu idan sukayi arba da abinda yake bayansu sai kaga sun kara zage damtse karfin gudun nasu ya karu fiye da na dazu Babu abinda zai bawo mutum mamaki face idan yaga yanda suke gudun sai ya rantse yace basu kasance bil adama ba kallo daya zakayi musu ka fahimci cewa sun kasance ya'yan wani hamshakin attajiri ko basarake saboda suturun dake jikinsu masu tsadar gaskene. Haka dai suka cigaba da gudu domin tsira da rayukansu daga sharrin abubuwan da suka biyo su babu alamun tsoro ko firgici a tattare da fuskokinsu har suka iso wani qasaitaccen birni ai kuwa sai suka kunna kai ta cikin wata yar mitsitsiyar taga ba tare sa sun jira masu gadin birnin sun bude musu kofar ba lokacin da abubuwan suka biyo yaran suka sauka a birnin nanfa jama'a suka dinga guje guje gamida iface iface kafin kace me gari ya kaure da ihun jama'a mutane suka ringa rugawa izuwa gidajensu suna debo makaman yaki a wannan lokacin sarkin dake mulki a birnin yana zaune akan karagarsa fadar ta qawatu ainun da kayan alatu nau'i nau' i daban daban dangin zinare da azurfa hardama abinda ido bai taba ganiba duk inda ka duba a fadar kawunan jama'ane rututu kamar dandazon kiyasai. . A gefe guda kuwa sarki SIYAMUL ANSAR na zaune akan kasaitaccen karagar mulki yana sanye da doguwar alkyabba akansa yana sanye da kambun mulki da aka sana'anta shi da zazzarar zinare da lu'u lu'u sarki siyamul ansar ya kasance dogon mutum mai qirar samudawan farko yana da kyakkyawar fuska da dan siririn gemu mai tsawon kamu biyu wanda shine ya kara fitar da kyawun fuskarsa kallo daya zakayi masa ka fahimci cewa ya kasance gwarzon jarumi yan majalisansa na zaune bisa shimfidu na alfarma wadanda idan mutum ya taka su saboda tsananin taushinsu sai yaji tamkar kafafunsa zasu nutse a ciki awannan lokaci babu abinda kunne keji face guje gujen jama'a da kuma shirun da ya wanzu a fada kamar mutuwa ta gifta sai can ga dakaru masu tsaron kofa sun shigo fadar hankalinsu a tashe. Koda ganin halin da suke ciki sai sarki ya dube su yace shin meke faruwa ne cikin rawar murya daya daga cikin dakarun ya budi baki dakyar yace ya shugabana muna cikin gudanar da ayyukanmu na tsaron kofa sai ga su yarima NAZMAR sun janyo mana wata gagarumar masifa bana tsammanin cewa akwai wata halitta da ta tsira da rayuwarta mu kanmu tsananin razana ya hana mu mu tantance wace irin masiface. Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa sarki siyamul ansar ya zare sharbebiyar takobi ya sare masa wuya nan take kan badakaren yayi fitar burgu daga gangar jikinsa jini yayi kwaranya kawai sai sarki siyamul ansar ya takarkare ya kwarara uban ihu wanda ya firgita gaba daya jama'ar dake fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin sai daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa nan take yayi umarni aka busa qahon yaki kafin wani lokaci mayaka sunyi cincirindo a kofar gidan sarauta shi ko sarki siyamul ansar sai ya shiga izuwa gidan sarauta jimm kadan sai ya fito cikin shigar yaki mai natukar kwarjini da ban tsoro. Fitowarsa da yan dakiku sai ga boka ZULWAL ya bayyana acikin shigar yaki ya fadi kasa yayi gaisuwa sarki ya dube shi tsananin fushi yana mai daka masa tsawa yace shin kana ina ne masifa tatunkaro kasata ka gaggauta nemo mana mafita domin tserar da ratukan al'ummar kasata cikin ladabi boka zulwal yace ya shugabana kayi sani cewa mafita dayace mafitar kuwa itace mu fita mu tari wannan masifar tun kafin ta iso birninmu ina mai tabbatar maka da cewa zamu samu nasara gama fadin hakan keda wuya sarki ya kada linzamin dokinsa ya shige gaba boka zulwal yabi bayansa take miliyoyin dakarun yaki sukayi koyi dashi sarki siyamul ansar bn fanan siri ya kasance mashahurin sarki kuma gagarumin attajiri da babu kamarsa a kaf nahiyar baitul wahir yana da matar aure guda daya kyakkyawar gaske mai suna NUZRA BIN SHA'ARAN a rayuwar sarki siyamul ansar babu wani rayuwar jin dadi da ya nema ya rasa face rashin haifuwa duk da irin tarin dukiya da karfin mulki da yake dashi ya tashi a banza domin bashida wanda zai gaji karagarsa Akalla ya ziyarci manyan bokaye sama da dari akan wannan matsala ta rashin haihuwa amma abu ya citra a wani shekara ne ya ziyarci wani boka acan birnin KUBA mai suna zulwal lokacin da sarki siyamul ansar ya bijirowa da boka zulwal da buka tunsa na rashin haihuwa sai kawai boka zulwal ya bushe da dariya har sai da ya fado daga kan kujerar da yake zaune kuma idanunsa suka ciko da kwalla al amarin da ya daurewa sarki siyamul ansar kai kenan kuma ya fusata ya dakawa boka zulwal tsawa yace dashi shin ina dalilin yin wannan dariya taka cikin nutsuwa da biyayya boka zulwal ya koma akan kujerarsa ya zauna yayi gyaran murya sannan ya fara magana karo na farko muryarsa mai kama da kukan jaki yana mai cewa asi ya huci zuciyarka ya sarkin sarakunan masu isa kayi sani cewa ba komaine ya sanya ni wannan dariya ba face bisa ganin yanda ka wahalar da kanka wajen fadin bukatar da take tafe dakai ya sarki mai cikakken iko kasani cewa tabbas ayanzu matarka na dauke da juna biyu nan bada dadewa ba zata haihu kuma ina mai farin cikin sanar dakai cewa 'ya'ya biyu zata haifa mace da namiji sai dai inda gizo ke sakar shine 'ya'yan da za a haifa maka zasu kasance hatsabibai marasa jin magana wadanda sune zasu zamo ajalinka. Yayin da boka zulwal yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki siyamul ansar ya dugunzuma fiye da kowane lokaci ya dubi boka zulwal yace ya sarkin bokaye shin babu wata hanya da za abi 'ya'yan da zan haifa basu kasance hatsabibaiba? boka zulwal ya nisa yace ai bakin alkalami ya bushe lallai wannan al amari haka zai kasance koda jn wannan batun sai sarki siyamul ansar ya sunkuyar da kansa kas yana mai zurfafa cikin kogon tunani abu na farko daya fado masa arai shine yanzu babu wata mafita face kayi murna da wadannan yara da za a haifa maka domin sune zasu gajeka bayan ranka tabbas bakada nadama koda sun zamo ajalinka ai da ace wani ne zai gaji karagarka gwara ace dankane na cikinka can kuma wata zuciyar tace ka cigaba da bincike ya za ayi ace 'ya'yan mutum sune zasu kasance ajalinsa lokacin da sarki Siyamul ansar yazo nan a tunaninsa sai ya dago da kansa ya dubi boka zulwal yace tabbas na amince 'ya'ya na su zamo ajalina matukar zasu gajeni bayan raina. Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar ya debi dukiya mai yawa ya bawo boka zulwal saboda tsananin murna sai da boka zulwal ya dinga birgima akasa tamkar wanda ya samu ciwon hauka domin tunda yake a rayuwarsa bai taba samun dukiya mai yawanta ba kumama yana da wani babban buri akan dukiyar yana son ya hada wani maganin tsafi da ita tun daga wannan rana sarki Siyamul ansar ya kasance cikin tsananin farin ciki kuma ya zamana dare da rana baya rabuwa da uwargidansa nuzra yana bata gudunmuwa wajen rainon juna biyun har ta sauka lafiya ta haifi 'ya'ya biyu kyawawa mace da namiji aka rada musu suna NAZMAR da HULAISA murna a wajen sarki kuwa ba a cewa komai domin a wannan rana ya dinga rabon dukiya da 'yanta bayi da barori sannan sai da akayi kwanaki ashirin ana shirya walimar farin ciki manyan sarakunan duniya sun sauka abirnin domin taya shi murna hakan ya sanya a wannan lokaci ko kasa mutum ya kasa sai an siya saboda kawai ana farin ciki kuma ya zamana sarki bashida wani abokin shawara face boka zulwal tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a jeba sai gashi kwance tashi Yarima nazmar da gimbiya hulaisa shekara uku a duniya kasancewar yanayin jikinsu irin na mahaifinsu ne sai ya zamana idan ka gansu lokacin da suka shekara uku sai kace sun shekara biyar da haihuwa. Tun suna wadannan shekaru suke nuna hatsabibancinsu domin basa iya zama waje guda ko an kulle su a daki sai sunyi dabaru sun fita awasu lokutan idan suka rasa hanyar da zasubi su fice daga gidan sarautar sai su hada rigima tsakanin dakarun dake tsaronsu sannan su sulale su fice daga sarautar domin akwai wani lokaci da sukaje suka tsokano wata qatuwar damisa ta biyosu har cikin gari ta dinga hallaka mutane sai dakyar da sidin goshi aka samu akayi maganin damisar kai in takaice maka kafin Nazmar da Hulaisa su shekara shida sun janyowa birnin masifu guda talatin kuma duk lokacin da hakan ya faru sai an samu salwantar rayuka da dukiyoyin al'umma wani abu da zai baka mamaki shine tunda aka haifi su yarima Nazmar arzikin kasar ya kara bunkasa amma sai dai mutane basu da kwanciyar hankali domin har kullum gani sukeyi su Yarima nazmar zasu janyo masifar da zata zamo ajalinsu ko asarar dukyarsu duk irin dakarun da sarki Siyamul ansar zai sanya domin tsaron su Yarima amma cikin hikima da basira sai Yarima nazmar sun samu nasarar gudowa shi kasansa sarki duk lokacin da ya tuna cewa su Yarima nazmar ne ajalinsa sai takaici ya turnuke shi har ya zubar da hawaye duk cikin mutanen birnin walau yan majalisa babu wanda ya iya kawowa sarki korafi su Yarima nazmar saboda ganin irin soyayyar da akeyi musu kuma babu wanda yake kaunar su domin ta sanadin su attajirai sun zamo talakawa wadansu sun zamo marayu. Duk lokacin da sarki ya samu labarin su Yarima nazman sun janyo wata masifa sai ya kara sanya matakan tsaro aturakarsa domin hanasu fita daga gidan sarautar. Lokacin da sarki Siyamul ansar da dakarun yakin suka fita daga kofar gari sai sukayi arba da wadansu irin jibga jibgan tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance suna da jiki irin na zaki amma kawunansu sun kasance na rakumin dawa suna dauke da kafafuwa guda shida akalla girman kowannensu yakai na qatuwar giwa fuka fukansu manya manya ne masu dauke da wadansu irin gashi mai kama da takobi awajen kaifi da tsini hakika ba karamin jarumi bane zaiyi arba wadannan tsutsaye face sai ya razana ainun yayi nadamar wamzuwarsa agaban kasa koda tsuntsayen su kimanin dubu sukayi arba da su sarki Siyamul ansar sai suka saki fukafukansu suka sauka aturba lokacin da dakarun sarki Siyamul ansar sukayi arba da wadannan tsuntsaye sai suka razana ainun da yawa daga cikinsu basu san sa adda suka saki fitsari a wandonsu ba kuma suka yunkura zasu koma da baya sai sarki Siyamul ansar ya daka musu tsawa suka tsaya cak jikinsu na tsuma gaminda karkarwa shi kansa sarki Siyamul ansar sai da yaji tsoro da razana sun darsu a zuciyarsa domin a iya tsawon rayuwarsa bai taba gani ko jin labarin tsuntsaye masu tsananin girma da ban tsoro kamarsu ba nanfa dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda tsananin dimauta su Yarima Nazmar kuwa lokacin da wadannan tsuntsaye suka biyo suka shiga birnin suka wuce kai tsaye izuwa turakarsu suka fara sharar bacci abinsu kai kace babu wani abu da ya faru agaresu al amarin da ya bawo kuyangi da barorin gidan sarautar mamaki kenan har wadansu suka raya zuciyarsu cewa anya kuwa su Yarima nazmar mutanene ba aljanu ba? ita kuwa mahaifiyarsu sai hankalinta ya dugunzuma ta kasa tsaye ta kasa zaune kawai sai ta dinga kai komo cikin turakar hawaye na zuba daga idanunta...... Zan Cigaba insha Allah Admin Dr. Goni S AbubakarKOGON ANNOBA Part B Littafi Na Daya 1 Marubucin Littafin Mansur Usman sufi Lokacin da aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Siyamul ansar da wadannan jibga jibgan tsuntsaye sai ya zamana babu wanda yayi yunkurin afkawo abokin gabarsa awannan lokaci gaba daya mayakan dake wajen hankalinsu atashe yake shi kansa sarki Siyamul ansar hankalinsa atashe yake fiye da kowa yayi karfin hali ne na irin masu manyan sarakuna koda sarki Siyamul ansar yaga tsuntsayen sunki yunkurin afka musu sai ya umarci wasu dakaru dari biyar da su dana bakarsu su harbawa tsuntsayen take dakarun sukabi umarnin suka dana bakarsu suka harbawo tsuntsayen yayin da kibiyoyi guda dari biyar suka sauka akan tsuntsayen sai akaga tsuntsayen sun tsaya cak ko gezau basuyi ba hasalima idan kibiyoyin suka sauka akansu sai dai tartsatsin wuta ya tashi kibiyoyin su zube kasa saida dakarun suka karar da kibiyoyinsu sannan tsuntsayen sukayi wani irin kuka mai firgita manyan jaruman duniya suka afka musu da yaki take tsuntsayen suka yanyame miliyoyin dakarun kamar yanda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro duk inda ka duba sune birjik babu abinda suke face hurowa dakarun wata dunkulalliyar wuta abakinsu ko su hallakasu da wadannan tsinin gashin dake fukafukansu masu tsananin kaifi da tsini. Cikin kankanin lokaci waje ya cikada ihun mazaje gamida karar karafkiya karafe gamida haniniyar dawakai mutuwar sadaukai ta cigaba da yawaita awajen nanfa aka kacame da azababben yayi tsakanin kowane bangare har yazama an shafe tsawon rabin sa'a su sarki Siyamul ansar basu samu nasarar kashe ko daya daga cikin tsuntsayen ba sai dai kaga tsuntsu ya wangame bakinsa ya hurawo badakare wuta sai dai kaga nan take badakare da dokinsa sun kama da wuta sassan jikin dakarun ya dinga shawagi a sararin samaniya kura ta turnuke kamar hadari ya gangamo akece da ruwan sama mala'ikan mutuwa ya wanzu yana shawagi asama dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu kai duk inda daya daga cikin tsuntsayen ya sanya gaba sai dai kaga dakaru suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe agonar auduga sarki Siyamul ansar ya wanzu yana kare kansa yana saran tsuntsayen cikin bakin zafin nama juriya da jarumtaka. Yayin da yaga yanda dakarunsa ke hallaka sai takaici ya turnuke shi ya takarkare ya kwarara uban ehu ya dire daga kan dokinsa ya tari wani tsuntsu guda daya suka kacame da yaki idan tsuntsun ya wangame bakinsa ya huro masa wuta sai kaga sarki Siyamul ansar ya kaucewa harin cikin bakin zafin nama idan wutar ta zuba a kasa sai kaga wajen ya haddasa wani wawakeken rami mai zurfin gaske Lokacin da tsuntsun yaga ya kasa samun nasara akan sarki Siyamuk ansar ta hanyar kone shi da wutar bakinsa sai kawai ya dinga kai masa yakushi da zaqo zaqon paratan hannunsa da nufin yayi fata fata da sassan jikinsa. Faruwar hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar ya fara gano lagon tsuntsun domin yanzu takobinsa ya fara tasiri akan tsuntsun dan ayanzu takobinsa na samun nasarar yankar jikin tsuntsun duk inda takobin ya sara ajikin tsuntsun sai dai kaga ya dare jinina kwaranya. Abangaren boka zulwal kuwa yana iyakar kokarinsa wajen yakar tsuntsayen amma babu abinda ya daure masa kai sama da yadda karfin sihiri baya tasiri ajikin tsuntsayen face tsagwaron karfin damtse duk inda mai kallo ya duba ba abinda zai gani face gawarwakin dakaru fululu kwance cikin jini wasu a babbake suna kauri jini kuwa ya cakude da kasa babu kyan gani ana cikin wannan yaki ne wannan tsuntsu ya samu nasarar yankar sarki Siyamul ansar da faratansa a cinya take inda ya yanke shi ya haddasa wani qaton rauni jini ya kwaranya saboda zafi da zugin da sarki Siyamul ansar yaji bai san sa'adda ya sandara uban ihu ba ya saki takobin dake hannunsa cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle daga inda yake tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan wuyan tsuntsun ya sanya hannayensa biyu ya kama kan tsuntsun ya murde iyakar karfinsa nan take wuyan ya karye ji kake rukuss sarki Siyamul ansar ya daka tsalle karo na biyu ya sauka daga kan tsuntsun take tsuntsun ya fadi kasa yiff tamkar an jefar da giwa ko shurawa baiyi ba. Yayin da tsuntsayen sukaga abinda ya faru ga dan uwansu sai gaba dayansu suka tsaya cak da yakin kawai sai suka bude fuka fukansu suka luluka sararin samaniya suna masu daukar gawar dan uwansu da sarki Siyamul ansar ya kashe koda bacewar tsuntsayen sai akaga sarki Siyamul ansar ya sulale kasa sumamme cikin tsananin kaduwa boka Zulwal ya ruga inda yake ya umarci dakaru su dauko shi aka shigar dashi cikin gidan sarauta bisa wani kasaitaccen keken doki lokacin da masu magani suka dukufa akan sarki Siyamul ansar domin ceto rayuwarsa sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ba tareda anga yayi wani kwakkwaran motsi ba al amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin masu maganin da boka Zulwal kenan kuma hankalinsu yayi mummunan tashi babu abinda yafi dugunzuma hankalinsu sai bisa ganin yanda raunin ciwon sarki Siyamul ansar din ke zubar da jini da ruwa mai doyin gaske kamar kurji yana zubar da mugunya duk kuwa da kasancewar masu maganin sunyi iyakar kokarinsu wajen bawa ciwon kariya da wadansu magunguna. A bangaren Nuzura kuwa lokacin da su yarima Nazmar suka farka daga baccinsu sukayi arba da mahaifiyarsu tana kaikomo acikin turakar hawaye na zuba daga idanunta sai suka rugo izuwa gareta suka fada kirjinta cikin matukar damuwa suka hada baki sukace ya ummanmu shin ina dalilin zubar da wannan hawayen naki koda jin wannan tambaya sai Nuzura ta kara kankame su ajikinta ta fashe da kuka a karo na biyu koda ganin hakan su Yarima Nazmar suka fashe da kukan sai da suka dauki tsawon lokaci suna cikin wannan hali sannan Nuzura ta janya jikinta daga nasu ta dube su cikin tsananin damuwa tace yaku 'ya'ya na kuyi sani cewa ba komai ne ya sanya ni zubar da hawaye ba sai bisa takaicin mugun halin da kuka jefa jama'ar wannan kasa da mahaifinku aciki kunsan cewa ba wannan ne karo na farko ba da hakan ya taba faruwa koda jin haka sai hawayen bakin ciki suka zubowa Nazmar da Hulaisa dukkaninsu suka budi baki sukace ki gafarce mu ya ummanmu tabbas mun aikata babban kuskure kuma munyi nadamar abinda muka aikata kafin su gama rufe bakinsu Nuzura ta tari numfashinsu tace wai shin ma in tambaye ku wane laifi kuka aikatawo wadannan tsuntsaye ina son ku sanar dani idan kuka boye mini gaskiya zan gudu in barku in tafi wata nahiya in cigaba da rayuwa har ajali ya riske ni. Yayin da su Yarima Nazmar sukaji abinda mahaifiyarsu tace sai idanunsu suka zazzaro suka shiga damuwa fiye da ko yaushe alamun rashin gaskiya karara ya baiyana a fuskarsu har Nazmar ya bude baki da nufin yace wani abu sai aka jiwo ihu da kururuwar sarki ta cika gaba daya gidan sarautar al amarin da ya sanya gidan sarautar ya hargtse da guje guje da iface ifacen jama'a Nuzura da su Yarima suka fice daga cikin turakar da sauri suka rugo izuwa turakar sarki cikin tsananin tashin hankali koda isowarsu izuwa turakar sai sukayi arba da sarki Siyamul ansar akwance cikin mawuyacin hali raunin cinyarsa na zubar da wannan ruwa mai doyin gaske koda shigowar su Yarima Nazmar sai kawai akaga sarki Siyamul ansar ya mike tsaye zumbur ya ruga inda suke ya rungumesu a kirjinsa al amarin da yayi matukar bawa masu magani mamaki kenan bisa ganin irin mugun raunin dake cinyarsa amma har ya iya taka kafarsa ba tare da an bawo masu maganin umarni ba suka fice daga turakar boka Zulwal yabi bayansu ya zamana saura su Yarima Nazmar da sarki Siyamul ansar kadai koda ficewarsu sai sarki Siyamul ansar ya kama hannun su Yarima Nazmar ya jasu har inda gadon sarautarsa yake ya zaunar dasu suka fuskanci juna sannan ya juya ya dubi uwargidansa Nuzura yana mai kura mata idanu yace ya abar kaunata bazakiyi farin ciki ba da 'ya'yanmu suka kasance cikin farin ciki da koshin lafiya. Koda jin wannan tambaya sai Nuzura taje ta zauna a bisa lumtsattsiyar kujera da take fuskantar su sarki Siyamul ansar ta dubesu cikin nutsuwa tace ya uban 'ya'yana kayi sani cewa ba komai ne ya sanya ni cikin halin rashin walwalaba sai bisa tsoro abinda su Yarima Nazmar suka janyo mana yanzu gashi sunyi sanadin yi maka mummunan rauni mutane da yawa sun rasa dukiyoyinsu da rayukansu ya zama wajibi ka tursasa su Yarima su sanar dakai laifin da suka aikatawa wadannan tsuntsaye sannan kuma a gano shin wanne irin tsuntsayene da matakin da ya kamata a dauka koda jin wadannan tambayoyi sai idanun sarki Siyamul ansar suka ciko da kwalla sannan ya budi baki cikin karfin hali yace tabbas maganarki gaskiyace ya uwargidana amma ki sani cewa matukar su Yarima na cikin koshin lafiya bana nadama don na rasa wata gaɓa ajikina har kullum tunanina shine wacce hanya zan bi domin ganin su yarima sun gajeni to amma idan su Yarima suka cigaba da janyo masifu a wannan birni hakan zai janyo rushewar birni gaba daya a doron kasa a kundin tarihin duniya Nuzura ce tayi wannan furuci ga sarki Siyamul ansar cikin tsananin damuwa shiru ne ya mamaye turakar na tsawon lokaci shigowar boka Zulwal itace ta kade shirun da ya wanzu a tsakaninsu boka Zulwal ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya dago da kansa cikin kakkausar murya yace ya shugabana kayi sani cewa bayan na fice daga wannan turaka na gudanar da bincike bisa halarar tsafi nan take na gano wani mummunar al amari cikin firgici sarki Siyamul ansar yace me ya faru ya dodon bokaye boka Zulwal ya hada fuska yace ya shugabana kayi sani cewa ba komai ne al amarin da nagani ba sai gameda wadannan tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance mallakin wani hatsabibin boka da ake yiwa lakabi da suna JABARUL SIHIR bokayen duniya sunyi ittifakin a wannan karshen qarni babu wata halitta mai tsananin zafin nama gamida karfin damtse tamkar wadannan tsuntsaye babban burin boka Jabarul sihir shine ya tsafance wani sihirtaccen kwai wanda daya daga cikin tsuntsayen ta haifa wanda da zarar kwan ya kyankyashe kansa zaiyiwa duniyar juyin mulki da wannan tsuntsaye bincike ya kara tabbatar mini da cewa maganin da zai warkar da su Yarima Nazmar yana cikin gidan Jabarul sihir wato ma'ul diya'u lallai ya zama wajibi a tura Yarima Nazmar su maidawa tsuntsayen abinda suka dauko musu domin ina mai tabbatar maka da cewa tsuntsayen zasu dawo wannan birni namu nan da wadansu kwanaki kasani cewa babu wata halitta da zata tsira daga cikin jama'arka matukar suka dawo. Koda jin wannan jawabi daga bakin Zulwal sai hankalin sarki Siyamul ansar ya dugunzuma ainun ya tashi ya dubi boka Zulwal yace shin kanada tabbacin cewa zamu iya zuwa gidan boka Jabarul sihir har mu debo ruwan ma'ul diya'u? wadanda zai warkarda su Yarima su daina rashin jin da sukeyi? boka Zulwal yace akwai wani jarumi mai suna HUZAIFAL BN MASNUR ma abocin addinin musulunci lallai kashe gari ya kamata mu gudanar da tafiya domin mu ziyarce shi domin ya amince da bukatarmu da wannan nakeyi maka bankwana na barka lafiya ya shugabana koda boka Zulwal ya gama wannan jawabi sai ya shafi kasa da hannunsa na hagu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen take sarki Siyamul ansar da Nuzura suka cika da farin ciki mara misaltuwa............... SHIN JARUMI HUZAIFAL ZAI AMINCE DA BUKATAR SARKI SIYAMUL ANSAR NA ZUWA GIDAN BOKA JABARUL SIHIR?. SHIN WANNE IRIN MUGUN TANADI BOKA JABARUL SIHIR ZAIYIWA SU SARKI SIYAMUL ANSAR?? SHIN WANNE IRIN MASIFU DA BALA'O'I NE KE TATTARE A FADAR BOKA JABARUL SIHIR.? Marubucin littafin yace mu hadu a KOGON ANNOBA na biyu don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Zan Cigaba insha Allah. Admin Dr. Goni S Abubakar.